An kashe mutum akalla 28 a Thailand bayan da wani tsohon dan sanda ya bude wuta a wata makarantar renon kananan yara.
‘Yan-sanda sun ce har yanzu ana neman dan-bindigar wanda ya aikata kisan a garin Nong Bua Lamphu da ke arewa maso gabashin kasar.
Bayanai sun nuna cewa yara da manya na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.
‘Yan-sanda sun ce maharin ya yi harbi tare da amfani da wuka wajen ta’asar, sannan ya tsere. Ba a dai san dalilin kai harin ba zuwa yanzu yayin da ake ci gaba da farautar mutumin.