Tsohon dan wasan tsakiya na Paris Saint-Germain, Modeste M’Bami ya mutu.
M’Bami ya mutu ranar Asabar yana da shekaru 40 bayan bugun zuciya.
PSG ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar yayin da suke ta’aziyya ga iyalan M’Bami.
“Paris Saint-Germain na cikin makoki. Modeste M’Bami ya rasu yana da shekaru 40 bayan ya yi fama da bugun zuciya.
Sanarwar kungiyar ta ce “Paris Saint-Germain tana mika ta’aziyya ga danginsa da masoyansa.”
M’Bami ya buga wa kungiyoyin Faransa da dama ciki har da PSG da Marseille.
Dan Kamarun ya lashe kofin Coupe de France da PSG a 2004 da 2006.
M’Bami ya kuma taka leda a Saudi Arabiya da China da kuma Spain kafin ya yi ritaya a shekarar 2016 bayan ya yi tazarce a Le Havre.