Tsohon dan majalisar dokokin jihar Kogi, Honarabul Christopher Atule Okoche, wanda ya wakilci mazabar Ibaji a karkashin jam’iyyar PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Okoche ya kuma kasance tsohon shugaban riko na karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi.
Ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Lahadi a karamar hukumar Ibaji.
Ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne bisa gagarumin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a matakin tarayya da kuma jihar Kogi.
Ya ce ya yi shawarwari da mutanen da ke kusa da shi kuma zai zo a ranar da aka ba shi tare da dukkan magoya bayansa zuwa APC.
Okoche ya ce babu tabbacin samun nasara ga jam’iyyar PDP ko wata jam’iyya a jihar Kogi baya ga jam’iyyar APC a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.


