Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa da mutuntawa suka cancanta, ba wulaƙanci ba.
Amnesty ta bayyana haka a shafinta na Facebook a yammacin ranar Lahadi, inda ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta girmama ƴancin da tsofaffin jami’an tsaron ke da shi na gudanar da zanga-zangar lumana saboda matsalar da suke fuskanta game da fansho.
“Matsalar da tsofaffin ƴansandan suke fuskanta a bayyane yake, kuma an daɗe ana watsi da ita. Wannan ya sa yin ritaya ya zama abin tsoro ga ƴansanda. Bayan ɗaukar lokaci suna aiki, tsofaffin ƴansandan da iyalansu na fama da abin da suka kira “biyan fansho na ganin-dama.”
“A watan Janairun shekarar 2025 ne aka biya wasu haƙƙoƙin tsofaffin ƴansandan baya sun yi zanga-zanga. Lallai ba ƙaramin abin kunya ba ne a ce sai sun yi zanga-zanga za a biya su haƙƙoƙinsu yadda ya dace. Dole gwamnatin Najeriya ta yi abin da ya dace wajen magance cin hanci a ya jefa tsofaffin ƴansandan nan cikin damuwa.