Tsofaffin sakatarorin tsaron Amurka biyar sun rubuta wasiƙa ga majalisar dokokin ƙasar inda suka yi Allah-wadarai da korar manyan jami’an ma’aikatar tsaro, inda suka kira matakin da rashin tunani.
Sun ɗauki matakin ne kwana ɗaya bayan da Shugaba Trump ya ƙaddamar da shirin korar manyan jami’an tsaron ƙasar tare da aniyar korar ma’aikata da dama a ƙasar.
A cikin wasiƙar, sakatarorin tsaron da suka yi aiki ƙarƙashin gwamnatin dukkan manyan jam’iyyun Amurka sun ce hakan wata alama ce da ke nuna alamar siyasantar da ɓangaren tsaron ƙasar.