Tsohon kwamishina da tsohon hadimin gwamna a lokacin mulkin PDP a jihar Gombe sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC .
Manyan jiga-jigan sun bayyana cewa, kyakkyawan jagorancin gwamna Inuwa Yahaya ne ya jawo hankalisu ga komawa APC.
Sun tabbatar da cewa za su ba da gudummuwar da ake bukata wajen cigaban jihar Gombe da APC.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi aiki da gwamnatin tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo.
Leadership ta rawaito cewa, manyan mutanen da suka sauya shekan sun haÉ—a da, tsohon kwamishina, Babagoro Hashidu, da tsohon mashawarci na musamman, Alhaji Maigari Malala.