Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su ministoci.
Cikin jerin har da Bello Matawalle, tsohon gwamnan Zamfara, da Atiku Bagudu, tsohon gwamnan Kebbi, da Gboyega Oyetola, tsohon gwamnan Osun.
Sauran tsofaffin gwamnonin sun haɗa da Ibrahim Geidam na Yobe, da Simon Lallong.