Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufa, ya kalubalanci magabatansa da su fito su rantse da Alkur’ani mai girma a matsayin hujjar cewa, ba su saci dukiyar al’umma ba a lokacin da suke kan mulki.
Gwamnan wanda ya zanta da Sashen Hausa na Kamfanin Yada Labarai na Jihar Kaduna, KSMC, ya yi ikirarin cewa galibin tsofaffin gwamnonin sun yi wa asusun gwamnati cikas a lokacin da suke mulki.
El-rufai zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas a mako mai zuwa.
Ya bayar da kalubalen ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ‘yan adawa ke yi na wasu manufofinsa, inda ya ce bai taba satar kudin gwamnati ba.
“Ban gina wani katafaren gida ba, bana bukata. Ban saci kudin kowa ba, ina kuma kalubalantar duk wanda ya yi mulkin jihar nan da ya fito ya rantse da Alkur’ani cewa, a lokacin da suke mulkin jihar ba su sace kobo da dukiyar Kaduna ba. hakki.
“Na rantse da Allah, zan yi wannan rantsuwa. Don haka, ina kalubalantar su duka. Ya kamata kowa ya fito ya fuskanci al’ummar jihar Kaduna ya ce musu bai wawure kudinsu ba,” inji shi.