Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce wasu tsiraru sun ƙwace iko da harkokin gwamnatinsa lokacin da yake mulki.
Buhari ya ce akwai tabbacin haka ta faru a tsawon mulkinsa na shekara takwas.
Idan za a iya tunawa, a 2016, uwargidan tsohon shugaban ƙasar, Aisha Buhari ta yi zargin cewa wasu tsiraru sun mamaye gwamnatin mijinta, sai dai Buhari ya ƙi gaskata hakan a lokacin.
Ya ƙara da cewa babu wanda ya taka doka kuma aka bari ya tafi ba tare da an hukunta shi ba