Wata kungiyar matasa karkashin kungiyar Asiwaju National Students Support Organisation (ANSSO), ta yaba da fitowar Asiwaju Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, tare da bayyana cewa, ci gaban zai kawo fata na karshe ga daliban Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a ta hannun kodinetan ta na kasa, Giwa Murtala Omatola-Moore, ANSSO ta taya tsohon gwamnan jihar Legas murnar ganin matakin farko na burinsa na zama shugaban tarayyar Najeriya.
Kungiyar ta bayyana cewa, nasarar da Tinubu ya samu ya kasance nasara ce ga adalci, daidaito, kebantaccen hali, cancanta da hadin kan kasa baki daya ga tarihin kasancewarsa Gwamna daya tilo da ya dauki ’yan Najeriya aiki a duk rarrabuwar kawuna ba tare da kabila, addini da yanki ba, don yin hidima a gwamnatinsa a matsayin Gwamnan Jihar Legas. In ji Independent.