Tsawa ta kashe wata yarinya ‘yar shekara 12 mai suna Maryam Rabi’u Garba, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a karamar hukumar Kaugama ta jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da yarinyar ke fakewa a cikin aji sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Ya ce, yarinyar za ta koma gida ne bayan mahaifiyarta ta aike ta da wani aiki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.


