Rundunar ‘yan sandar jihar Jigawa, sun kama wani magidanci ɗan shekara 40, bisa zargin kashe ɗiyarsa ta cikin sa a ƙaramar hukumar Babura.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shitu, ya fitar da sanarwar aranar Alhamis a Dutse, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Ya ce lamarin ya faru ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022 a ƙauyen Achiya, bayan mutumin ya shararawa yarinyar yar shekara 11 mari mai suna Salima Hannafi.
Ya ƙara da cewa, sanadin wannan marin da ya mata, yarinyar Salima Hannafi, ta rasa rayuwarta a wurin da ya mare ta.