Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Tinubu ya faɗi haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasar na ranar murnar cikar ƙasar shekara 63 da samun yancin kai.
Ya ce za su kare rayukan ƴan ƙasar ne ta hanyar tabbatar da jami’an tsaro sun yi aiki tare da kuma tattara bayanan sirri.
Shugaban na Najeriya ya kuma ce an ɗora wa hafsoshin tsaro nauyin karfafa wa jami’ansu gwiwa wajen aiki tare.
“Ina jinjina tare da yaba wa jami’an tsaronmu kan yadda suke ba mu tsaro. Da yawa sun sadaukar da rayukansu don kare ƙasarmu. Muna tunawa da su a yau da kuma iyalansu.
Tinubu ya ce za a wadata sojoji da kayan aikin da ake buƙata domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.