fidelitybank

Tsaro: ‘Yan Najeriya ku hada kai domin kawo karshen ta’addanci

Date:

Mai martaba Sarkin Musulmai, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, ya shawarci ‘yan Najeriya da su hada kai, domin kawo karshen ta’addanci a Najeriya.

Sultan ya furta hakan ne a taron majalisar hadin kan addinai ta (NIREC), ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai musamman Musulmi da Kirista za su rinka zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Mai martaba Sultan, ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jam’a ke ci gaba da kamari a Najeriya, amma kuma Musulmi da Kirista sun bige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

Ya kuma ce,”Dole ne mu daina zargin juna, kuma mu hada kai, domin mu yaki makiyan mu, idan na ce zan yi magana kan rashin tsaro a Arewa babu lokacin da za mu bar dakin taron nan”. A cewar Sultan.

Ya kara da cewa, “Yan kwanakin da suka wuce mun karanta a jaridu yadda aka kona matafiya a bas a Sokoto. Babu ranar da za ta zo ta wuce ba a kashe mutane a Arewa ba, musamman Arewa maso Yamma”.

Bugu da kari, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci shugabanni da sauran hukumomin tsaro su hada kai su kuma fahimci girman matsalar tare da magance ta. Inji BBC.

 

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp