Masarautar Katsina ta kori wani babban ɗan majalisar masarautar, Makaman Katsina Alh. Idris Sule kan zargin hannu wajen rashin zaman lafiya a yankinsa
A wata wasiƙa da fadar ta aike wa hakimin mai ɗauke da sa hannun Kauran Katsina Aminu Nuhu Abdulkadir ta ce an kori Makaman Katsina ne bayan da aka same shi da laifi kan zargin da mutanensa suke yi masa da hannu wajen kawo rashin zaman lafiya a yankinsa.
Masarautar ce ta bisa ga takardar da ta samu daga ofishin gwamantin jihar, wadda a cikin gwamnan jihar ya tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa hakimin bayan ƙorafe-ƙorafen da ya samu.
”Dan haka Masarautar Katsina ta yanke shawarar sallamarka a matsayin Makaman Katsina”, kamar yadda wasikar ta nuna.
Korarren Makaman ya shiga cikin jerin masu riƙe da sarautun gargajiya a yankin arewa maso yammacin ƙasar da aka tuɓe musu rawani sakamakon alaƙa da ayyukan ‘yan bindiga, da rashin zaman lafiya a yankin


