fidelitybank

Tsaro: Buhari ya tura tawagar manyan jami’an tsaro zuwa Sokoto da Katsina

Date:

Tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke fuskanci kakkausar suka daga wajen al’umm, a kan harin da ‘yan ta’adda suka kai na kona matafiya 42 kurmus a Sabon Birni da ke Sokoto, a daidai wannan lokacin Buhari ya fusata ya aike da tawagar manyan jami’an tsaro zuwa yankin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da tawaga mai karfi zuwa jihohin Katsina da Sokoto domin dakile ta’addancin da ke ta karuwa.

Cikin wata sanarwar da Buhari ya yi ya ce,”Na aika da wata tawaga ta manyan jami’an tsaro da na leken asiri karkashin jagorancin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, zuwa jihohin Sokoto da Katsina, a matsayin martani ga karuwar ayyukan ‘yan ta’adda a jihohin biyu”.

“Ina tsammani daga gare su rahoton halin da ake ciki nan da nan da kuma shawarwari game da ayyukan da za a bi, domin magance wannan yanayin. Ba za mu bar wata kafa ba a yunkurin tabbatar da tsaron rayuwar al’ummar Najeriya, a duk inda suke a kasar nan. Duk abin da a ke bukata za a yi shi, har sai an samu cikakkiyar nasara”. A cewar Buhari.

Sauran ‘yan tawagar tsaron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, Darakta-Janar na Hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban tsaro Jami’in leken asiri, Manjo Janar Samuel Adebayo.

 

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp