Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya koma jam’iyyar Labour Party, kwanaki kadan bayan ficewa daga babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party.
Peter Obi ya ce jam’iyyar ita ce tsarin da ya dace da burinsa.
A baya Peter Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, wanda ya ficce ganin cewar, kamar ba za a yi masa adalci ba wurin tsayar da dan takara.