fidelitybank

Tsantsar talauci ne ke jawo rashin tsaro a Arewa – Uba Sani

Date:

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce, tsansar talauci da koma bayan tattalin arziki su ne manyan abubuwan da ke haifar da masaloli tsaro a yankin arewacin Najeriya, inda ya yi gargaɗin cewa muddin ba a magance su gaba ɗaya ba to yankin zai ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankaln.

Gwamnan ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa na Sunday Politics na gidan talibijin na Channels, inda ya ce gwamnatinsa ta soma ne da fito da hanyoyin yaƙi da talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa, inda ya alaƙanta hakan ga irin ƙwarewar da ya ya samu lokacin da ya ke shugaban kwamitin da ke lura da bankuna na majalisar dattawan a lokacin yana ɗan majalsar dattawan.

“Lokacin da aka zaɓe ni a matsayin gwamnan Kaduna, abinda na soma yi shi ne duba girman matsalar talaucin da ake fama da ita, ba wai a jihata kaɗai ba a’a duka yankin arewa. Na taɓa riƙe muƙamin shugaban kwamitin da ke lura da harkokin bankuna na majalisar dattawa. Ina da bayanai da dukan alƙalumman da aka tattara daga Sashen Bunƙasa Babban Bankin Najeriya (CBN). Ina mai tabbatar maka cewa girman talaucin da ake da shi a shekarar 2023, lokacin da muka zo ya kai wani matsayi mai muni” in ji gwamnan.

A cewar sa fiye da kashi 60 zuwa 65 cikin ɗari na mutanen arewacin Najeriya – musamman a shiyar arewa maso yamma – na fama da tsananin talauci a lokacin da ya zama gwamman jihar Kaduna.

Uba Sani ya ce hakan na iya sa matasa da dama su shiga aikin ta’addanci kasancewar ƴanbindiga za su iya ɗaukar su haya domin kai hare-hare.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp