Akalla mutum 124 sun rasa ransu sakamakon tsananin sanyi a Afghanistan a makonni biyu da suka gabata, a cewar jami’an Taliban.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Agajin ƙasar , ya ce sama da dabbobi 70,000 ne kuma suka mutu a wani yanayi na tsananin sanyi da ba a ga irinsa ba cikin shekara goma.
Kungiyoyin bayar da agaji da dama sun dakatar da ayyukansu a baya-bayan nan bayan haramta wa matan ƙasar aiki da kungiyoyi masu zaman kansu da Taliban ta yi.
Wani minista a gwamnatin Taliban ya ce duk da samun waɗanda suka mutu, ba za a janye haramcin ba.
Muƙaddashin Ministan Agaji, Mullah Mohammad Abbas Akhund, ya faɗawa BBC cewa dutsar kankara ta mamaye yawancin yankuna a ƙasar, inda aka aike da jirage masu saukar ungulu don zuwa ceto mutane, sai dai, jiragen basa samun damar sauka a yankuna da ke da tsaunuka ba.