Tsohon gwamnan jihar Kano kuma wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Sanat Rabi’u Kwankwaso, ya ce babu komai tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba gida-gida sai bayar da shawara.
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da BBC, lokacin da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa cewa shi yake juya akalar gwamnatin Abban.
Kwankwaso ya ce “ko ɗanka ba za ka je ka zauna ƙofar ofishinsa ba ka ce kai za ka riƙa fada masa abin da zai yi”.
Ya kuma ce ya zuwa yanzu babu wata yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin tarayya kamar yadda ake yaɗawa.
Kazalika ya bayar da martani kan adawat da take tsakaninsa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar ta Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce duk abubuwan da ke tsakaninu “ban taba yin wani abu domin cutar da Ganduje ba, amma komai mutum ya shuka shi zai girba” in ji Kwankwaso