Tsagin Sanata Ibrahim Shekarau a jihar Kano, ya yi fatali da yunkurin sulhun da uwar jam’iyyar APC ke kokarin musu da tsagin Ganduje.
Shekarau ya zargi uwar jam’iyyar da rashin adalci a yayin sulhun, ya ce, hakan bai dace ba. A cewar Shekarau, sun fara ganin takardar sanarwar sulhun da za a yi ne a kafafen sada zumunta tun kafin ta iske su.
A wata tattaunawa da BBC ta yi bayan fitar sanarwar uwar jam’iyyar, Sanata Shekarau ya ce sun yi fatali da sanarwar kuma ba su aminta da ita ba.
Shekarau ya kara da cewa, a sanarwar jam’iyyar, ba ta yi magana kan matsayar da bangarorin 2 suka cimma ba, kuma jam’iyya ba ta fadi komai da bangarorin suka bukata ba.
Shekarau ya ce, abu na 2 kafin fitar takardar, an kai wa Ganduje takardar kafin a kai masa wanda hakan bai dace ba. Ya kara da cewa, takardar ta shiga duniya inda a ka ganta a kafafen sada zumunta kafin a kawo masa.