Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben 2024 na jamâiyyar Republican.
Trump na neman komawa fadar White House bayan da ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2020 ga Joe Biden.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a gidansa da ke Mar-a-Lago, Florida.
“Don sake mayar da Amurka girma da daukaka. A daren yau ne nake sanar da cewa zan tsaya takarar shugabancin Amurka,â in ji Trump.
Ku tuna cewa Trump ya lashe zaben shugabancin Amurka a karon farko a shekarar 2016 lokacin da ya fafata da Hillary Clinton.
Trump zai zama shugaban kasa na biyu da zai sake karbar mulki a fadar White House idan ya yi nasara a shekarar 2024, inda ya zama shugaban kasa na 45 da na 47.