Donald Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa zai rattaba hannu kan wasu jerin umarni na zartarwa a ranarsa ta farko a matsayin shugaban Amurka.
Daga cikin matakan da ya ce zai akwai waɗanda za su shafi shige da fice ba bisa ƙa’ida ba, da daƙile ƙa’idojin muhalli da kuma kawar da manufofin bambance-bambance daga aikin soja.
A lokacin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayansa, a wani gangami a birnin Washington a jajibirin rantsar da shi karo na biyu, Mista Trump ya kuma yaba da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Gaza, yana mai cewa hakan ta faru ne kawai albarkacin nasararsa.
Shi ma hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya hau duro ya yi jawabi a taƙaice yana mai cewa martaba da buwayar Amurka na daf da dawowa a idon duniya.