fidelitybank

Trump zai kakaba sabon haraji ga kasashen duniya

Date:

Shugaban Amurka Donald Trump zai sanar da sabbin harajin a yayin wani jawabin da zai yi a lambun Rose da ke fadar White House a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne a yayin da kallo ya koma Amurkan, inda duniya ke sauraron abin da sanarwar za ta ƙunsa, ganin tawagar da ke aiki da shugaban ƙasar sun yi gum a kan bayanai game da sabbin harajin.

A watan Maris ɗin da ya wuce, Mista Trump ya ce sabbin harajin za su zama tamkar rama wa kura aniyarta ne, don haka Amurka za ta sanya harajin daidai da yadda ƙasashe suka sanya mata.

Yayin da daga bisani kuma ya nuna cewa harajin zai iya zama ƙasa da abin da ƙasashe ke cajin Amurka.

Sai dai babu tabbacin taƙamaimai waɗanda harajin zai shafa, ko zai zama bai ɗaya ga kowa.

Sai dai akwai sabon haraji na kashi 25 cikin ɗari, a kan motoci da za a shigar Amurka wanda zai fara aiki a ranar Laraba.

Yayin da kayan motoci suma za su fuskanci irin wannan harajin a cikin watanni masu zuwa.

Tuni Amurkar ta fara aiwatar da wasu sabbin harajin a cikin watan Maris, kamar wanda ya shafi ƙarafa da goronruwa ko sanholo da ake shigarwa ƙasar.

Inda ƙasar ta ɗaga harajin zuwa kashi 25 cikin ɗari. Kuma tuni ta ƙara haraji kan duka kayayyakin da China ke shigarwa Amurkar, zuwa kashi 20 cikin ɗari.

Ƙasar Canada ta rama abin da Amurka ta yi mata, inda ta sanya harajin kashi 25 cikin ɗari kan ƙarafa da sanholo.

Yayin da China ta rama, inda ta kai harajin shigar mata da wasu kayan gona daga Amurka ke yi, zuwa kashi 10- 15 cikin ɗari.

Tarayyar Turai ta yi gargaɗin ɗaukar matakan ramuwa, yayin da Burtaniya ta ce tana jiran duk abin da Amurkan za ta yi.

Amma ranar wanka ba a ɓoyon cibi, domin a yau Amurkar za ta sanar da sabbin harajin da za ta sanya wa abokan hulɗarta na kasuwanci.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp