Daya daga cikin martanin da mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta yi bayan muhawarar da aka tafka tsakanin tsohon shugaban kasar Donald Trump da Joe Biden shi ne Trump “ba zai bayar da tartibiyar amsa ba kan ko zai amince da sakamakon zabe.”
Duk da tambayar da yar jarida Dana Bash da ta jagoranci muhawarar ta yi ta yi masa kan ko zai amince da saKamakon zaben watan Nuwamba, Trump ya yi shakulatun bangaro.
A yunkuri na uku kuma sai Trump ya kada baki ya ce zai amince da sakamakon “idan har aka yi zabe sahihi mai nagarta”.
Tsohon shugaban kasar ta Amurka ya kuma sake nanata ikirarinsa mara tushe na batun yin magudi a zaben da aka yi a 2020.