Kotun ƙolin Amurka ta garƙame ƙofar duk wani yunƙuri na Colorado na cire sunan Donald Trump a cikin takardun kada ƙuri’a na zaɓen fidda gwani na ƴantakarar shugaban ƙasa.
Haka kuma hukunci ya sahfi sauran jihohin da ke da aniyar ɗaukar irin wannan mataki, ko duk wani yunƙuri da haramta masa takara.
Hukuncin kotun ya ce majalisar dokokin ƙasar ce kalai ke da alhakin cire sunan tsohon shugaban a kan takardar kada ƙuri’a kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi wa garambawul na 14 ya tanada.
Mista Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, yana mai cewa:”wannan kyakkyawar rana ce ga Amurka.”
Hakan babbar nasara ce ga Donald Trump, amma hukuncin ya zo ne a makon da ya ke da shari’o’in zargin aikata laifuka.
Kotun kolin ta yi watsi ne da hukuncin da babbar kotun Colarado ta yanke na hana Trump tsayawa takara saboda goyon bayan harin da magoya bayansa suka kai majalisar dokokin Amurka a shekarar 2021.