fidelitybank

Trump ya yi barazanar daina bai wa Afirka ta Kudu tallafi

Date:

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, zai katse duk wani tallafi da ƙasarsa ke bai wa Afirka ta kudu bisa zargin ta da kwace filaye da kuma nuna wariya ga wani ɓangare na al’umma.

A watan da ya gabata ne Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanya hannu kan wani ƙudirin doka da ya ba da damar kwace filaye ba tare da biyan diyya ba a wasu lokuta.

A shafinsa na Truth, Trump ya ce ”zan katse duk wani tallafi ga Afirka ta kudu har sai an kammala gudanar da cikakken bincike kan lamarin.”

A cewar alƙaluman gwamnatin Amurka, ƙasar ta ware dala miliyan 440 domin tallafi ga Afirka ta kudu a shekarar 2023.

Sai dai wasu masu fashin baƙi na nuna fargaba kan mummunar sakamakon da dokar za ta iya samarwa kwatankwancin yadda aka samu a Zimbabwe wadda kwace filaye ya yi sanadin ruguza tattalin arziƙin kasar ya kuma kori masu zuba jari.

Batun mallakar filaye matsala ce da ta daɗe tana damun Afirka ta kudu ganin cewa fararen fata ne ke cigaba da mallakar akasarin gonaki a ƙasar, shekaru 30 bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata. In ji BBC.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp