Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa Trump ya “yaudari” ɗaukacin Iran da kuma al’ummar Amurka.
Abbas ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Istanbul lokacin da yake mayar da martani kan hare-haren da Amurka ta kai.
“Yayin da aka zaɓi Trump don kawo karshen shigar Amurka cikin yake-yake a sassan duniya, ya yaudari Iran ta hanyar take tsarin diflomasiyya har ma da waɗanda suka zaɓe shi ta hanyar miƙa kai don shiga yaƙi, inda ya gwammace ya saka rayuwar ƴan ƙasar cikin masifa da kuma kashe dukiyar Amurka don cimma burin gwamnatin Isra’ila,” in ji Araghchi.