Shugaba Trump ya ce, ya umarci a matsar da wasu jiragen ƙarƙashin teku masu ɗauke da makaman nukilliya guda biyu kusa da Rasha, a matsayin martani ga abin da ya kira “wauta da tsokana” kan kalaman da tsohon shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya yi.
Mutanen biyu sun jima suna sukar juna kai-tsaye a shafukan sada zumunta.
A saƙon da ya wallafa na baya-bayanan, Mista Medvedev ya ce barazanar da Amurka ke musu na tsaurara takunkumai saboda yaƙin Rasha da Ukraine takalar gagarumin yaƙi take yi.
Sai dai wakilin BBC ya ce, shugaba Trump na kaffa-kaffa wajen bayyana ko hakan na nufin zai yi amfani da makaman nukilliya.
A ranar Juma’a shugaba Putin ya nuna cewa babu wani abu da ya sauya kan sharuɗan na zaman lafiya da Ukraine.