Hukumar Tsaron Amurka FBI ta tabbatar da cewa an yi yunkurin hallaka tsohon shugaban kasar Donald Trump.
Wani dan bindiga ne ya bude wuta a wurin yakin neman zaben tsohon shugaban kasar Donald Trump.
Ba a san dalilin maharin na son kashe tsohon shugaban ba, kana ba a sanar da sunansa ba har kawo yanzu.
Hotunan da aka yaÉ—a a Internet sun nuna lokacin da Donald Trump ya sunkuya cikin gaggawa ya buya a karkashin abun magana, yayin da yake tsaka da jawabi a kan duro.
Nan da nan jami’an tsaro na yan sanda da wadanda ke ba shi kariya suka kewaye shi suka yi masa rumfa, daga bisani suka fice da shi a gaggauce.
An fita da shi yana takawa dakyar, jini na zuba a kunnensa da fuskarsa.
Magoya bayansa sun rika yarda allunan goyon bayansa suna ranta a na kare, wasu na kwantawa a kasa don kare kansu.
Cikin yan mintuna kalilan wurin ya watse baki daya.
A cikin wata sanarwa da hukumar kare fararen hula ta kasar ta fitar, ta ce Trump na cikin koshin lafiya kuma an kare rayuwarsa.
Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka ana gudanar da bincike mai zurfi kuma za a fitar da karin bayani idan an samu.
Shugaba Biden ya bayyana a gaban manema labarai a mahaifarsa ta Delaware, inda yi Allah wadai da harin, yana cewa zai yi magana da abokin hamayyar na sa, domin taya shi alhini. In ji BBC.
Tuni suma yan siyasa daga jam’iyyar tsohon shugaban kasar Trump ta Republican har ma da abokan hamayyarsa na Democrats suka fara yin tir da harin, suna kuma addu’ar samun sauki da nuna goyon baya ga tsohon shugaban.


