Ɗan takarar shugaban Amurka na jam’iyyar Repblican, Donald Trump ya cigaba da sukar da yake yi a kan birnin Springfield na Ohio, tare maimata zarginsa cewa baƙin-haure sun karɓe ikon harkokin birnin.
Tsohon shugaban ƙasar ya soma irin waɗannan zarge-zarge ne tun lokacin da ya yi iƙirarin a lokacin muhawarar da ya tafka da Kamala Harris cewa baƙi ‘yan Haiti na cinye karnuka da kyanwoyin mutane
Magajin garin ya buƙaci Mista Trump ya daina irin waɗannan kalamai.
Robert Rue ya shaida wa BBC cewa kalaman Trump sun tilasta kashe ƙarin kuɗaɗe wajen tabbatar da tsaro saboda barazanar harin bam da ya biyo baya.
Wannan yanayi a yanzu ya tilasta rufe makarantu da gine-ginen gwamnati.