fidelitybank

Trump ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani duk da haramcin kotu

Date:

Donald Trump ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar Republican a New Hampshire yayin da yake neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar.

Sakamakon kusan rabin kuri’un da aka kirga ya ba shi fiye da kashi hamsin da biyar cikin dari, yayin da abokiyar hamayyarsa da ta rage, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, ta samu kusan kashi arba’in da uku cikin dari.

Kuma ta lashi takobin ci gaba da neman takarar.

Yanzu dai an kirga sama da rabin kur’un zaben fid da gwanin na jihar ta New Hampshire, inda daman kamar yadda aka yi hasashe wanda zai yi nasara, tsohon shugaban Amurkar, Donald Trump yake gaban abokiyar hamayyarsa, guda daya tilo tsohuwar jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Nikki Haley da kusan maki 10.

Akwai dai wakilai ko delegets, 22 a jihar, inda kafar yada labarai ta CBS, da ke mu’amulla da BBC a Amurkar ta yi hasashen cewa Trump zai samu akalla 12 daga ciki, yayin da Haley za ta samu akalla tara idan ta yi kokari, hakan zai sa Trump ya samu jumulla 32 kenan Haley ta kasance da 17.

Wanda zai zama gwani a zaben dai dole ne ya kasance ya samu deleget 1,215.

Zuwa yanzu dai Mista Trump ya kama wannan hanya ba ji ba gani , kuma nasara ce ga tsohon shugaban na Amurka da za ta kara masa karfi na zama dan takarar jam’iyyar Republican a babban zaben kasar a watan Nuwamba.

Tuni daman ya gabatar da jawabin nasara har sau biyu a cikin kwana 8. Sai dai kalamansa ga taron magoya bayansa a New Hampshire a wannan karon bayan ganin ya kama hanyar nasara sun kasance daban da wadanda ya yi ranar Litinin a Iowa.

A baya ya nuna muhimmancin hadin kan jam’iyyarsu tare da yaba wa abokan takararsa to amma a wannan karon ya caccaki abokiyar hamayyar tasa ne, Nikki Haley da ta rage, wadda ta yi jawabi ga magoya bayanta jim kadan kafin Trump ya shiga fage ya gabatar da nasa jawabin, inda ya ce tana magana kamar ita ce ta ci zaben.

Ya ce “dole in gaya muku abin ban sha’awa ne, saboda na ce, kai wannan irin nasara, to amma sai kawai wani ya shigo fagen ya yi kwalliya da kyau, a lokacin ana kan bakwai, to amma yanzu na shigo an ce 14. Amma ita ta shigo a lokacin ana bakwai, to amma dole ne mu yi abin da ya dace ga jam’iyyarmu,

Ta dage da, tana jawabi, na ce kai, kamar ta yi nasara, ba ta ci ba, ta fadi.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp