A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar da cewa shugaba Donald Trump na fama da rashin lafiya a jijiyoyinsa na ƙafa da ke haddasa jiyoyin gaza aikewa da jini zuwa zuciya, abin da ke sa jini ya taru a ƙafar ta kuma kumbura.
A yayin taron manema labarai da aka saba yi, sakataren watsa labaran fadar ta White House ya ce mista Trump mai shekaru 79 ya fahimci kumburi a ƙafafunsa abin da ya sa likitansa yin nazari kuma ya gano cewa cutar ɗaukar jini zuciya da jiyoyin ƙafafun suka gaza ce.
Hotunan baya-bayan nan sun nuna yadda aka ga Trump da ɗaure-ɗaure a bayan hannunsa. Fadar White House ta ce ɗaure-ɗauren da aka gani a bayan hannun shugaban ba su da alaƙa da cutar gaza kai jini zuciya da jiyoyin nasa ke fuskanta, inda fadar ta ce hakan ya faru ne sakamakon yawon gaisawa da jama’a.