fidelitybank

Trump ya na dagula mana lisafi – Hamas

Date:

Shugabannin ƙungiyar Hamas sun ce, tsoma bakin da Donald Turmp ke yi a baya-bayan nan game da Gaza na ƙara dagula batun yarjejeniyar tsagaitar da ke rawa da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu.

A jiya Litinin Trump ya yi barazanar watsi da yarjejeniyar matuƙar Hamas ta gaza sakin ɗaukacin ƴan Isra’ila da take garkuwa da su.

Ɗaya daga cikin masu magana da yawun Hamas, Sami Abu Zuhri ya ce hanya ɗaya tilo ta tabbatar da cewa dukkanin waɗanda ake garkuwa da su sun koma gida ita ce ta hanyar martaba yarjejeniyar da aka cimma a watan jiya sau-da-ƙafa.

A jiya Litinin, Hamas ta yi barazanar jinkirta sakin sauran ƴan Isra’ila da take riƙe da su bisa zargin Isra’ilar da rashin martaba ƙa’idojin yarjejeniyar yadda ya kamata.

Hujjojin da Hamas ta bayar sun haɗa da cewa Isra’ila na yin cikas ga shigar kayan agaji zuwa Gaza da kuma sakin Falasɗinawan da ke hannunta.

Isra’ila ta yi watsi da zargin, sannan tana ƙara yawan dakarunta a kusa da yankin.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp