Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya miƙa kansa ga hukumar gidan yari na Fulton a jihar Georgia inda aka ɗauki tambarin yatsu da hotonsa.
Ya Shaida wa ‘yan jarida a wajen gidan kaso da ke jihar Georgia, tuhume-tuhumen da ake masa karya ce tsagwaron ta.
Ana tuhumar da yunƙurin sauya sakamakon zaɓen jihar, da ta da zaune-tsaye da tunzura magoya bayansa yin bore a majalisar dokokin Amurka.
An dai bayar da belinsa kan dala dubu 200. Amma ya barin wurin sai ya wallafa hotonsa da aka dauka a gidan yarin, tare da rubutu a ƙasa “Karka taba miƙa wuya”.


