Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa ƙasashen ƙungiyar tarayyar turai da Mexico garajin kashi 30 na kayayyakinsu.
Trump ya ce harajin zai fara aiki ne daga watan Agusta mai zuwa, sannan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda koma-baya da ake samu na harkokin kasuwanci da ƙasashen tarayyar da kuma zargin da ya yi cewa Mexico ta ƙi ɗaukar mataki kan ƙwayar fentanyl.
Ƙasashen tarayyar guda 27 ne suka fi gudanar da hada-hadar kasuwanci da Amurka, inda ta ce tana da yaƙinin za su samu fahimtar juna da Washington kafin wa’adin na Agustan.