fidelitybank

Trump ya janye kudurinsa na janye hannun Amurka daga hukumar mu – WHO

Date:

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira ga Amurka da ta janye ƙudurinta da ficewa daga cikin harkokin hukumar.

Hukumar ta bayyana haka ne a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce tana taka rawa wajen inganta lafiya da tsaron al’umma, ciki har da Amurka.

“Ta hanyar gano musabbabin cututtuka da inganta asibitoci da ganowa tare da kiyaye aukuwa ko yaɗuwar cututtuka ciki har da annoba.”

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka na cikin ƙasashen da suka assasa hukumar a shekarar 1948, kuma tun a lokacin take taimaka wa ayyukan ƙungiyar tare da sauran mambobin hukumar guda 193.

A sama da shekara 70 da hukumar ke aiki, WHO da Amurka sun ceci rayuka da dama da ba za a iya ƙididdigewa ba, sannan ta kare yaɗuwar cututtuka da dama a ƙasashen duniya ciki har da Amurka.

“Ta hanyar wannan haɗakar, muka yaƙi cutar smallpox, sannan muna gab da yaƙar polio. Wannan ya sa muke fata Amurka za ta sake tunani, tare da janye ƙudurinta na ficewa daga hukumar ta lafiya domin kula da lafiyar miliyoyin mutane a duniya.”

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp