Jami’an gwamnatin Amurka sun ce shugaba Trump ya ba da umarnin dakatar da duk wani agajin soji da ake bai wa Ukraine.
Matakin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan cacar bakin da Mista Trump ya yi da shugaba Zelensky a fadar White House.
Ana tunanin umarnin – wanda zai fara aiki nan take – zai shafi makamai da alburusai na miliyoyin daloli da aka ware don kai wa Ukraine a cikin kwanakin karshe na gwamnatin Biden.
Tun da farko a jiya Litinin Shugaba Trump ya caccaki Mista Zelensky a bainar jama’a – yana mai cewa ba zai daɗe a kan karagar mulki ba idan har bai goyi bayan yarjejeniyar zaman lafiya ba.