Amurka ta dakatar da agajin da ta ke bai wa Afirka ta Kudu, daidai lokacin da zaman tankiya ke ƙaruwa kan dokar filaye.
Shugaba Trump na Amurkan ne ya bayar da umarnin, saboda zargin sabuwar dokar, ta bai wa gwamnati damar karɓe gonakin Turawa farar fata ba tare da biyan diyya ba.
Sai dai gwamnatin Shugaba Cyril RamaPhosa ta ce Afrika ta Kudu ba za ta amince a yi mata barazana ba.
Shi ma makusancin Mista Trump, kuma haifaffen Afirka ta Kudun, Biloniya Elon Musk, ya soki matakin na Afirka ta Kudu.
A ƙarshe umarnin shugaban ƙasar ya soki Afirka ta Kudu kan ƙarar da ta shigar gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC kan kisan ƙare dangin da Isra’ila ke yi a Gaza.