Donald Trump ya soki Kamala Harris a yaƙin neman zaɓensa na farko tun bayan da ta zama ƴar takarar da ake kyautata zaton za ta yi wa jam’iyar Democrat takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba.
Yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a jihar California, ɗan takarar jam’iyar Republican ɗin, ya kira abokiyar hamayyar tasa da mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka mafi rashin cancanta a tarihi.
Ya kuma soki manufofinta na ƴancin zubar da ciki da kuma haƙƙin mallakar bindiga, ya kuma ce ta gaza a ɓangaren baƙin haure.
Ya ce Kamala Harris ta kasance a matsayin jigon bala’o’in da Biden ya haddasa.


