Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon Musk, kwana guda bayan hamshaƙin attajirin ya sanar da cewa zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Mista Trump ya ce Elon Musk ya bauɗe hanya.
”An gina tsarin siyasar Amurka kan aƙidar tsarin jam’iyya biyu”, in ji Shugaba Trump, yana mai cewa ƙarin jam’iyya zai haifar da ruɗani a siyasar Amurka.
Shi dai Elon Musk ya ce jam’iyyar America Party da yake yunƙurin kafawa za ta ƙwato wa masu zaɓe ƴancinsu.