Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya caccaki magajinsa Joe Biden kan kujerar da aka ba shi a zaman da ya yi a jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
An yi jana’izar marigayiyar shugabar Burtaniya da na Commonwealth a ranar Litinin a gidan ajiyar kaya na Royal Vault da ke Windsor Castle.
Trump ya yi ba’a game da matsayin Biden a cikin jerie na 14 da ya zauna a Jana’izar a Westminster Abbey.
Trump ya ce da ya na kan karagar mulki da ba zai faru ba hakan.
Babban hamshakin dan kasuwa mai shekaru 76 da haifuwa yayi tsokaci akan dandalinsa na zamani tare da hoton shugaban kasar Amurka.
“Wannan shi ne abin da ya faru da Amurka a cikin ‘yan shekaru biyu kawai. Babu girmamawa! Duk da haka, lokaci ne mai kyau ga shugabanmu ya san shugabannin wasu Æ™asashen duniya na uku.
“Idan ni ne shugaban kasa, da ba za su dawo da ni can ba – kuma kasarmu za ta bambanta da yadda take a yanzu!” ya rubuta.