A karon farko tun bayan samunsa da laifi, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a gangamin yakin neman zabe.
Da yake yi wa dandazon magoya bayansa jawabi a Arizona, Mr Trump ya caccaki alkalin da ya jagoranci shari’ar, da caccakar Shugaba Biden kan dokar shige da fice.
Donald Trump ya jima yana magana kan masu Æ™etara iyakar Amurka daga Mexico ba bisa ka’aida ba, inda ya ce zai dawo da dubban sojin Amurka da ke Æ™asashen waje domin magance matsalar.
Cikin wata 2 da ya gabata, Mr Trump ya yi ta zarya a kotunan Amurka kan laifuka daban-daban.