Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nemi gidan Talabijin na CNN, da ya biya shi diyar dala miliyan dari hudu da saba’in da biyar.
Trump ya dai zargi sanannen gidan talabijin din na Amurka da bata masa suna ne, wanda ya ce, sun kwatanta shi da Adolf Hitler na Jamus.
Akan haka tsohon Shugaban Amurkar ya, Trump ya maka CNN a kotu, bisa zargin sun bata masa suna.
Donald Trump ya shigar da kara mai shafi 29 a wata kotu da ke Florida, inda yake zargin CNN da ƙoƙarin yi masa maƙarƙashiya.
Sai dai har yanzu gidan talabijin na CNN din bai mayar da martani ba kan zargin na Trump.