Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da naɗin manyan muƙaman gwamnatinsa.
A ranar Juma’a Mista Turm ya sanar da naɗin ‘yar majalisa Republican, Lori Chavez-DeRemer a matsayin sakatariyar ƙwadago.
Sai kuma tsohon dan gidan Dave Weldon da ya naɗa shugaban hukumar lafiya matakin farko.
Shi kuwa Dr Marty Makary ya samu muƙamin kwamishinan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna.
Mista Trump ya kuma zaɓi tsohon ɗan ƙwallon Amurka Scott Turner a matsayin sakataren gidaje da birane da karkara.