Shugaba Biden ya kara zage dantse wajen sukar tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ake sa ran zai yi wa jam’iyyar Republican takara a zaben shugaban kasar da ke tafe.
A yayin da yake yunƙurin sake farfado da yakin neman zabensa a wani gangami a Detroit, Mista Biden ya kira Trump a matsayin wanda ya riga rana faduwa.
Da dama na kallon kalaman na sa a matsayin wani ƙi faɗi, da kuma son nuna yana nan da ƙarfinsa yayin da ƴan jam’iyyarsa ke ta kiran ya koma gefe ya haƙura da takara.
Ya fito ƙarara ya shaida wa masu irin wannan kira cewa babu inda zai je.
Ya ce ‘’nine ɗan takarar jam’iyyar Democrat, kuma mutum na farko a tarihi a Democrat da Republican da ya taɓa kayar da Donald Trump.’’
Yana magana ne kwana guda bayan da wani babban ƙusa a jam’iyyar ta Democrat a majalisar wakilan ƙasar Jim Clybur, ya buƙaci masu irin wannan kira su mayar da wuƙarsu cikin kube.


