Iran ta musanta alaka da yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Ofishin Jakadancin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce zargin yunkurin kashe Trump “ba shi da tushe balle makama.”
Wani matashi dan shekara 20 ya harbe Trump a yunkurinsa na kashe shi a lokacin yakin neman zabensa a Butler da ke jihar Pennsylvania a ranar Asabar.
Yayin da mai harbin ya kusa harbe Trump, ma’aikatar sirri ta kashe matashin mai shekaru 20 a wurin.
Bayan faruwar lamarin, an zargi Iran da yunkurin kashe Trump a matsayin martani ga kisan Janar Soleimani.
Sai dai Ofishin Jakadancin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana Trump a matsayin mai laifi wanda za a hukunta shi ta hanyar doka.
Rundunar ta kuma ce dan bindigar mai suna Thomas Matthew Crooks, ba shi da wata alaka da kasar ta.
“A mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Trump ya kasance mai laifi wanda dole ne a gurfanar da shi tare da hukunta shi a gaban kotun shari’a saboda ba da umarnin kashe Janar Soleimani.
“Iran ta zabi hanyar doka don gurfanar da shi a gaban shari’a,” in ji shi.