fidelitybank

Trump da Putin za su gana tsawon sa’o’i biyu

Date:

Shugaban Amurka, Donald Trump, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, za su yi ganawar sa’o’i biyu daga karfe 9 na safe.

Kakakin Kremlin Dimtry Peskov ya sanar da hakan a ranar Talata.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar Rasha RIA, Peskov ya ce shugabannin biyu za su tattauna kan Ukraine da kuma “kara daidaita alakar kasashen biyu”.

Ya bayyana cewa tattaunawar da ta gabata tsakanin Shugaba Trump da Putin na nufin “akwai wata fahimta”.

Jaridar DAILY POST ta bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Amurka na kokarin kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki 30 a yakin da Rasha ke yi da Ukraine.

Shugaba Trump ya yi imanin cewa tsagaita bude wuta na kwanaki 30 za ta kasance kofar cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin a kasashen biyu da ke gaba da juna.

Shugaba Putin ya bayyana wani kyakkyawan fata amma ya ce Rasha na da tambayoyin da ba a amsa ba.

Sai dai Ukraine ta amince da kudurin tsagaita bude wuta a taronta da Amurka a Saudiyya amma kuma ta nuna shakku kan hakikanin manufar Rasha.

the nation newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp