Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan inganta ayyukan gwamnatin ƙasar, Elon Musk, ya ƙara zafafa sukar da yake yi wa sabon ƙudirin haraji da kashe kuɗaɗen gwamnati da shugaban ƙasar ya gabatar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar dattawa ke ci gaba da kada ƙuri’a kan sauye-sauyen da ake son yi wa dokar.
Elon Musk ya yi Allah-wadai da ƙudirin, yana mai cewa babu hankali ko tunani a cikinsa.
Ya kuma yi barazanar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a matsayin martani kan lamarin.
’Yan jam’iyyar Democrat na ƙoƙarin ganin cewa wannan ƙuri’ar ta kasance mai wahala ga ’yan jam’iyyar Republican da ke goyon bayan ƙudirin.
Shugaba Trump na fatan sanya hannu kan ƙudirin dokar kafin ranar Juma’a mai zuwa.