Arsenal ta tabbatar da daukar Leandro Trossard daga Brighton.
Kungiyoyin Premier biyun, sun amince da yarjejeniyar fan miliyan 27 kan dan wasan mai shekaru 28.
Trossard ya kammala gwajin lafiyarsa tare da Gunners a yau kuma an dauki hotonsa yana atisaye tare da sauran ‘yan wasan Mikel Arteta.
Arsenal, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ta lura: “An gabatar da dukkan takardu, muna fatan Leandro Trossard zai kasance a shirye don zaba gabanin wasan da Manchester United.”
Trossard, wanda zai iya taka leda a gaban uku, zai sanya riga lamba 19 a Arsenal.